Posts

Showing posts with the label sanya idanu

Hajj2023: Kungiyar Hajj Reporters Ta Samar Da Wata Tawaga Da Zata Sanya Idanu Kan Aikin Hajjin Bana A Kasa Mai Tsarki

Image
Kungiyar 'yan jaridu masu daukar rahotannin aikin ta kasa (IHR) ta samar da wata tawaga mai mutane 5 da za ta sanya ido kan ayyukan da  jami’an aikin hajji da aka nada da masu ba da hidima ga alhazan Najeriya a kasar Saudiyya. Tawagar za ta yi aiki tare da kwamitin tantancewa da hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) kamar yadda shugaban hukumar ta IHR Ibrahim Muhammad ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis. Kungiyar farar hula mai zaman kanta ta ce an kafa wannan tawaga ne domin tabbatar da cewa dukkan jami’an sun gudanar da ayyukan da aka ba su kamar yadda aka tsara a jadawalin ayyukansu. Tawagar za ta kuma tabbatar da cewa masu ba da hidimar da suka tsunduma aikin yi wa alhazan Najeriya hidima a fannonin masauki, sufuri, ciyar da abinci, tsaftar muhalli, tantuna a Muna da Arafat sun gudanar da ayyuka masu inganci ta hanyar samar da ingantattun ayyuka ga mahajjatan Najeriya. Tawagar dai za ta kasance karkashin jagorancin Kodinetan IHR na kasa Ibrahim Muhamm...