Tinubu Ya Yi Alawadai Da Harin 'Yan Bindiga A Zamfara, Kano Da Katsina is a Tare Da Jajantawa Wadanda Abun Ya Shafa
Tinubu ya kuma yi ta'azziya ga iyalan Abacha da na Sheikh Gumi Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara da kuma garin Maigari na karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano a karshen mako. Rahotanni sun ce an kashe jami’in ‘yan sanda na Dibision (DPO), sufeto ‘yan sanda da dan banga a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara. A harin na Kano wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun shiga gidan wani basarake inda suka harbe shi har lahira. A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar a ranar Litinin, Tinubu ya ce harin da aka kai a garin Maru bayan an samu zaman lafiya a jihar Zamfara, abin tunatarwa ne cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya. “A matsayinmu na kasa dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan ‘yan kasuwa na mutuwa da ta’addanci gaba daya, kashe-kashe...