Kotun Koli Ta Ba Wa Rufai Hanga Na NNPP Kujerar Sanatan Kano Ta Tsakiya

Kotun Koli ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, a matsayin wanda ya ci zaben Sanatan Kano ta Tsakiya. Kotun ta umarci INEC ta maye gurbin Shekarau da sunan Rufai Hanga a matsayin halastaccen wanda ya ci zaben kujerar a karkashin Jam’iyyar NNPP. Ta kuma tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta tabbatar da Rufai Hanga a matsayin halastaccen dan takarar NNPP a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Maris. INEC dai ta bayyana Shekarau a matsayin wanda ya ci zaben duk kuwa da cewa ya sauya sheka daga NNPP zuwa PDP kuma ya sanar da cewa ya janye daga takarar . AMINIYA