Posts

Showing posts with the label Bazoam

Mun Dakile Yunkurin Bazoum Na Tserewa Daga Nijar Zuwa Najeriya - Sojoji

Image
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da daƙile wani yunƙurin hamɓararren Shugaban ƙasar Mohamed Bazoum na tserewa tare da iyalinsa. Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya yi wa jama’ar ƙasar ta Talabijin, ya ce Bazoum da iyalinsa sun tsara guduwa daga Fadar Shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe uku na dare. Martanin tubabbun ’yan Boko Haram kan tuban muzuru Kamfanin Nokia zai sallami ma’aikata 14,000 saboda rashin ciniki Ya ce Mohamed Bazoum ya yi kokarin tserewa da karfe 3 na safiyar ranar Alhamis tare da iyalansa masu dafa masu abinci 2 da kuma jami’an tsaro guda biyu. Sai dai a cewar sojojin, wannan yunƙurin da bai kai ga ci ba, na cikin wani tsari da aka shirya da kuma sojojin suka ce suke bi sau da kafa. Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce “matakin farko na wannan shiri shi ne na su fice daga cikin fadar zuwa kewayen wurin inda wata mota ke jiransu daga nan ne za a dauke su zuwa wani gida da ke cikin unguwar...