Search This Blog

Showing posts with label IPMAN. Show all posts
Showing posts with label IPMAN. Show all posts

Tuesday, 7 February 2023

Dillalan Man Fetur Sun Lashe Amansu Kan Shiga Yajin Aiki

Yan sa’o’i bayan umartar mambobinta su rufe ilahirin gidajen man fetur a Najeriya, Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta bukaci a bude gidajen a ci gaba da sayarwa.

Aminiya ta rawaito yadda a ranar Talata kungiyar ta bukaci a rufe ilahirin gidajen man da ke kasar nan take sannan a fara yajin aiki, kamar yadda wata sanarwa da Shugaban kungiyar na kasa, Mohammed Kuluwa, ya fitar ranar Talata.


IPMAN ta ce, “Sakamakon mawuyacin halin da muka tsinci kanmu a ciki wajen samo man da kuma sayar da shi da tsada, da kuma yadda hukumomi ke tilasta mana sayar da shi a kan farashin da muke faduwa.

“Muna umartar ilahirin mambobinmu da su dakatar da sayar da mai, sannan su dakatar da biyan kudin duk wani man da suka riga suke kokarin sarowa daga yanzu har sai abin da hali ya yi.”


To sai dai ’yan sa’o’i bayan waccan sanarwar, IPMAN ta yi mi’ara koma baya.

“Bayan tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki, muna umartar gidajen mai da su bude su ci gaba da sayarwa, yayin da uwar kungiya za ta ci gaba da tattaunawa,” kamar yadda sabuwar sanarwar ta IPMAN, wacce ita ma Shugaban nata ya sanya wa hannu ta fada.

Sanarwar ta dillalan man na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da dogayen layuka da wahalar man ta haifar a fadin kasar.

Kazalika, ana fama da tsadar man a kusan duk fadin kasar, inda a wasu wuraren ya haura N370 a kan kowacce lita, yayin da a wasu Jihohin kuma rahotanni suka ce har ma ya haura N400

Hakan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da karancin takardun kudi sakamakon canjin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

(AMINIYA) 

Thursday, 12 January 2023

Za a shafe wata shida nan gaba cikin karancin Fetur a Najeriya - Inji IPMAN

Kungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a faɗin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Kungiyar ta ce wahalhalun ko karancin na da alaƙa da shirin gwamnati na janye tallafin mai baki daya a cikin watan Yuni.

Tun a shekarar da ta gabata al'ummar kasar ke fama da karanci mai a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewaci.

A ranar Litinin ministan albarkatun fetur, Timipre Sylva, ya ce kamfanin mai na NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu.

A makon da ya gabata, ministan kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ya ce gwamnatin Tarayya ta ware naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...