CBN zai hukunta wasu bankuna a Kano kan sabbin kuɗaɗe
Babban bankin Najeriya CBN ya ce zai dauki tsattsauran mataki kan wasu bankuna a Jihar Kano, saboda kin zuwa su karbi sabbin takardun naira da ya samar. CBN reshen Jihar ta Kano ya jaddada matsayarsa kan cewa cewa karshen watan nan na Janairu zai daina karbar tsaffin kudaden kamar yadda ya sanar tun bara. Al'umma a fadin Najeriya na ta kokawa kan karancin sabbin kudaden da CBN ya kaddamar a bankuna, baya ga korafin da suke yi na rashin bayar da cikakken wa'adi domin mayar da tsofaffin kudaden bankuna. Shugaban CBN reshen Jihar Kano Malam Umar Ibrahim Biyu a tattaunawarsa da BBC ya ce, akwai isassun sabbin takardun kudaden bankuna kawai ake jira su je su karba. "Mun yi magana da bankuna kan cewa su aiko mana da adadin kudin da suke bukata da za a zuba a na'urar ATM domin amfanin yau da gobe ga al'umma. "Haka muka shaida musu, kuma tuni mun fara bayarwa. Sai dai korafe-korafe sun mana yawa kan ba a samun wadannan kudade a bankuna. "Wannan dalili ne ya sa ...