MARTANI GA MAWAKI DAUDA RARARA - Bashir Ahmad
Na kalli wani bangare na videon da yake yawo na taron manema labarai da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gabatar a yau, musamman bangarorin da ya ci wa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari mutunci tare da zargin cewa sai da ya rusa kasar baki daya kafin ya bar mulki. Bayan kammala kallon video na yi yunkurin bawa Rarara amsa daya bayan daya ga duk wadannan zarge - zargen da yayi, sai dai daga bisani da na sake yin nazari a tsanake sai na ga babu bukatar hakan a halkance da kuma mutunce, saboda wasu dalilai kwarara guda biyu. Na farko, cikin videon, Rarara yayi ikirarin cewa wai gudunmawar daya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai bawa kan sa irin wannnan gudunmawa ba. IKON ALLAH. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana? Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a bashi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a bawa mukaman na ministoci. TASHIN HANKALI. Ko akwai chemis...