Wa’adin Tsofaffin Kudi: Mun Zuba Ido Mu Ga Yadda CBN Zai Kare Da Mutanen Karkara —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) bai sanya su cikin masu ruwa da tsaki ba kan batun sauya fasalin takardun kudi, dalilin ke nan da suka zuba ido su ga yadda zai kare da mutanen karkara idan wa’adin karbar tsohuwar naira ya cika.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin Babban Jami’in Gudanarwa na CBN shiyyar Sakkwato, Dahiru Usman hadi da wasu jami’an babban bankin ranar Alhamis a fadarsa.

Alhaji Bako Zuntu ya riga mu gida gaskiya
Duk da gargadin CBN har yanzu bankuna na bai wa mutane tsohuwar naira ta na’urar ATM
Abubakar ya ce kamata ya yi a ce CBN din ya sanya dukkanin masu ruwa da tsaki tun a matakin farko na sauya takardun na naira, amma sai ya yi biris da sarakunan gargajiya.

“Akwai mutanen karkarar ma da ba su san an sauya kudin ba kwata-kwata, kuma idan ka ba su sabo ba za su karba ba saboda za su zaci na bogi ne.

“Mu ne muke kusa da su, mu ne kuma ke da hanyoyin isar musu da sakon, don bibiyar kafafen yada labarai ba dabi’ar mutanen karkara ba ce.

“Amma da muka ga ba a saka mu a lamarin ba, sai muka koma gefe mu ga yadda za a kare idan wa’adin karbar tsofaffin kudin ya cika.

“Duk da haka muna rokon CBN ya kara duba wa’adin da ya bayar, domin rashin tsaro na daga cikin dalilan da suka sa mazauna karkara ke tsoron dibar kudi masu yawa su kai bankuna, gudun yi musu fashi a hanya ko ma sace su gaba daya,” in ji shi.

A nasa bangaren, Babban Jami’in na CBN ya ce sun kawo ziyarar ce domin sanar da Sarkin a hukumance cewa an sauya takardun kudin, da kuma neman shawarwarinsa.

Ya kuma yi alkwarin isar da sakon Sarkin ga shalkwatar CBN din da zarar sun kammala zagayen duba yadda bankuna a jihar ke bayar da sababbin takardun kudin da suka je yi.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki