Posts

Showing posts with the label Amurka

Gwamna Yusuf Ya Isa Kasar Amurka Domin Halartar Taro Da Gwamnonin Arewa

Image
Gwamnan jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya isa kasar Amurka domin halartar babban taron tattaunawa da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya. A sanarwar da Darakta Janar Mai kula da harkokin yada labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace taron na kwanaki uku da gwamnonin Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Plateau ke halarta, an shirya shi ne domin magance matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya da kuma mafi kyawun zabi na dakile kalubalen. HaÉ—in kai mai zurfi zai baiwa Gwamnonin wasu jihohin da ke fama da rikici zurfafa fahimtar yanayin barazanar tsaro, yanayin tattalin arziki, da kuma damar da za a yi kusa da shi don samar da kwanciyar hankali a Arewacin Najeriya. Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka kuma za ta fadada ilimi kan karfafa rigakafin rikice-rikice a yankin, ta hanyoyin da ba na tashin hankali ba na shigar da kungiyoyin da ke dauke da makamai a matsayin madadin warware rikici. Shirin d...

Shugaba Biden ya bayyana aniyar sake tsayawa takara

Image
  Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara a zaÉ“en shekara ta 2024, inda mai yiwuwa ya sake takara da Donald Trump. An yi tsammanin jam'iyyar Democrat za ta sake neman wa'adin mulki na biyu tsawon shekara huÉ—u tare da Æ™addamar da yaÆ™in neman zaÉ“ensa a wani bidiyo ranar Talata. Ya ce wannan muhimmin lokaci ne da zai sake bayyana aniyrasa ta sake neman mulkin Amurka. Mataimakiyar shugaban Æ™asar Kamala Harris, mai shekaru 58, ita ma ta nuna aniyar sake zama abokin takararsa. Mista Biden, mai shekaru 80, shi ne shugaban Æ™asa mafi tsufa a tarihin Amurka, kuma da alama zai fuskanci tambayoyi kan shekarunsa a tsawon lokacin yakin neman zaÉ“e. Zai kasance mai shekara 86 bayan kammala wa'adinsa na biyu a mulkii cikin shekara ta 2029. BBC Article share tools

An Kama Donald Trump Kan Zargin Aikata Laifuka

Image
An kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump kan zargin aikata laifuka. An kama shi ne ranar Talata yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan. An tsare ‘yan sandan da suka yi sanadin mutuwar matashi a Filato ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagaci da danta a Kano Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alakar nema a tsakaninsu lokacin da yake takarar shugaban kasa a zaben 2016. Shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taba kamawa a tarihin kasar. To sai dai, a lokuta da dama Trump ya musanta zargin. Sai dai Trump ya ce duk wadanan tuhume-tuhumen da ake masa ba komai ba ne face yi wa takararsa ta neman wa’adi na biyu zagon kasa. AMINIYA 

Yau sabuwar majalisar Amurka za ta yi zamanta na farko

Image
A yau Talata sabuwar majalisar dokokin Amurka za ta fara aiki inda dan Republican Kevin McCarthy zai nemi zama shugaban majalisar wakilai. Bayan zaben rabin wa’adi da a aka yi a watan Nuwamba, ‘yan Republican sun karbe ragamar shugabancin majalisar wakilai amma da dan kankanin rinjaye. Majalisar dokokin Amurkar a wannan ta rabu gida biyu, inda ‘yan Democrat suka ci gaba da rike shugabancin majalisar dattawa yayin da ‘yan Republican suke karbe majalisar wakilai. Wani abu da zai fi jan hankali a yau shi ne yadda ‘yan Republican za su zabi shugaban majalisar ta wakilai. McCarthy na fatan ganin ya gaji Nancy Pelosi ‘yar Democrat amma kuma yana fuskantar kalubalen rashin samun goyon baya - har daga abokansa. Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 100 da dan takarar neman shugabancin majalisar wakilai ya gaza samun goyon baya daga wasu ‘yan jam’iyyarsa. Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan McCarthy. Dan majalisar wakilai Andy Riggs na jihar Arizona da Steve Scalia ...

2023: Amurka Za Ta Mara Wa Najeriya Baya A Harkar Zabe

Image
Gwamnatin Kasar Amurka ta ce za ta mara wa Najeriya baya dangane da zaben 2023 don tabbatar da masu kada kuri’a sun samu aminci a yayin zaben. Amurka ta bayyana hakan ne ta bakin ofishin jakadancinta a Najeriya. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito Amurka za ta mara wa kasar baya ne karkashin shirin ‘Vote023’. Vote023 shiri ne na musamman don wayar da kan jama’a kan harkokin zabe musamman ganin yadda zaben 2023 ya karato. Daya daga cikin jagororin shirin ‘Vote023’, Misis Angela Ochu-Baiye ce ta bayyana haka ranar Asabar a Legas. Ochu-Baiye ta ce abin a yaba ne ganin Ofishin Jakadancin Amurka ya amice su yi aiki tare don wayar da kan ’yan kasa kan zaben 2023.
Image
Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya nemi jin matsayin shari'a daga babbar kotun duniya kan mamayen da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasɗinawa. Ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƙasa 87, sai 26 suka nuna adawa da shi ciki har da Amurka da Burtaniya. Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya tana da ƙarfin yanke hukunce-hukuncen da wajibi ne a yi musu biyayya, amma ba ta iya tilasta aiki da su. Ƙuri'ar ta ranar Juma'a, ta zo ne kwana ɗaya bayan rantsar da Benjamin Netanyahu a matsayin firaminista na gwamnatin Isra'ila mafi tsaurin ra'ayi a tarihi. Isra'ila ta mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma ko da yake ta janye daga Gaza amma har yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya tana kallon yankin a matsayin wanda ke ƙarƙashin mamaye. Isra'ila na iƙirarin cewa gaba ɗayan Ƙudus ne babban birninta, yayin da Falasɗinawa ke cewa Gabashin Ƙudus ne babban birnin wata ƙasarsu da za a kafa nan gaba. Amurka na cikin tsirarun ƙasashen da suka amince da Ƙudus a matsayin babban b...

Mutane sama da 20 ne suka mutu saboda tsananin sanyi a Amurka

Image
  Fiye da Amurkawa 200,000 ne suka wayi gari ba tare da wutar lantarki ba a safiyar ranar Kirsimeti sakamakon guguwar sanyi da ta shafe kwanaki ana tafkawa a wasu jihohin gabashin Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20 Matsanancin sanyi, dauke da guguwa mai cike da tarihi ya mamaye  jihohin Amurka 48 a wannan makon, abin da ya haifar da cikas ga matafiya da dakatar da zirga-zirgar dubban jirage, inda dubban gidaje ke cike da dusar kankara. An tabbatar da mutuwar mutane 22 a jihohi takwas, ciki har da akalla mutane bakwai da suka mutu a yammacin New York, inda dusar kankara dauke iska mai tsanani suka mamaye garuruwa. Shugaban gundumar Mark Poloncarz ya shaida wa manema labarai cewa, "Muna da mutane bakwai da aka tabbatar sun mutu sakamakon guguwar da ta afku a gundumar Erie. Wasu ma'aurata a Buffalo, wanda ke kan iyaka daga Canada, sun shaidawa AFP cewa tsananin sanyi ba zai basu damar tafiyar tsawon minti 10 ba na ziyartar danginsu a bikin Kirsimeti. Haka ...