Waiwaye Adon Tafiya: Daya Daga Cikin Dalilan Da Suka Sa Muke Yakar Yin Zanga-zanga A Kano - Farfesa Salisu Shehu
A shekarar 2003 ne Amerika ta jagoranci mamaye Kasar Iraqi . Wannan aiki na zalunci da ta'addanci ya tunzura Kasashen Musulmi wanda ya sa aka rinka ZANGA-ZANGA da kona tutar Amerika a kasashen Musulmi baki daya. KUMA abin lura da izina shi ne duk wadannan ZANGA-ZANGA basu hana Amerika yin ta'addancin da ta yi niyya ba. Bil hasali ma kara maimaitawa take ta yi, WAMA LIBYA, WA SIRIYA , BI BA'ID. Wannan dalili ya sa mu ma a Kano aka shirya lacca ta musamman a Masallacin Umar ibn Al'-Khattab (Dangi) wacce kusan dukkan manyan Malamanmu na Kano kamar su Sheikh Isa Waziri, Sheikh Ibrahim Umar Kabo, Sheikh Dr. Aminuddeen Abubakar, Sheikh Ja'afar, Sheikh Yahaya Faruk Chedi , etc Rahimahumullahu duk sun halarta. Daga nan Masallacin aka yi jerin gwano cikin lumana aka bi State Road aka je gidan Gwamnati aka mika takarda ta yin Allah wadai da Kasar Amerika, aka bukaci Gwamnatin Jihar Kano ta isar da takardar ga Ofishin Jakadancin Amerika . Daga nan aka dawo Masalla