Posts

Showing posts with the label Alan Waka

Aminu Alan Waka ya ajiye takarar sa ya fice daga jam’iyyar Sha’aban Sharada

Image
Bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADP Shahararren mawakin nan wanda kuma ya shiga siyasa Aminu Ala, ya fice daga Jam’iyyar ADP ta Sha’aban Sharada ya kuma koma jam’iyyar APC. KADAURA24 ta rawaito cewa Alan Waka dai yana daga cikin ‘yan Kannywood da suka shiga tafiyar Sha’aban Sharada, Inda har ma ya rabauta da takarar dan majalisar tarayya na karamar hukumar Nasarawa a jam’iyyar ADP bisa jagorancin Dauda Kahutu Rarara. Jim kadan bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADP, Kadaura24 ta gano Alan waka tare da mataimakin gwamnan kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna wanda Kuma shi ne dan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyar APC, hakan Kuma ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar marawa Gawuna baya.  Hakan dai na alamta cewa Alan Waka ya koma tafiyar jam’iyyar APC Kuma zai marawa takarar Dr. Gawuna bayan maimakon ta Sha’aban Sharada da ya faro. Ku biyo mu nan gaba kadan idan mun tattauna da Aminu Alan zaku ji cikakken bayani kan dalilansa na ficewa daga tafiyar Sha’aban Sharada zuwa APC ...