Najeriya Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Da Saudiyya



 Najeriya ta samu nasarar yin taro da hukumomin aikin hajji na Saudiyya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin bana.

Karamin ministan wajen Najeriya Ambasada Zubairu Dada ne ya jagoranci tawagar Najeriya wajen kulla wannan yarjejeniya da ke zama ka’idar amincewa kowace kasa ta kawo alhazai.

Rattaba hannu kan yarjejeniyar ya biyo bayan wata ganawa ta yanar gizo tsakanin shugaban hukumar Alhazan Zikrullah Kunle Hassan da hukumomin aikin hajji na Saudiyya a watan Disambar bara.

Kwamishinan ma’aikata da tsara manufofi na hukumar Alhazan Nura Hassan Yakasai wanda ke cikin tawagar ya bayyana cewa Saudiyya ta amince da dawowa da Najeriya yawan kujeru na asali da ta ke samu mutum dubu 95.




Hakanan Yakasai ya ce a yanzu ba dogon bincike kan cutar korona bairos matukar maniyyaci ya na da shaidar gwajin cutar.

Malamai sun shiga fadakar da maniyyata don kara fahimtar dokokin aikin da zummar samun ladan wankuwa daga zanubai.

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci kara karfafa koyar da maniyyatan aikin daga Najeriya har zuwa Makkah da Madina.


A shekarun baya ‘yan Najeriya kan saye dukkan kujerun aikin hajji har ma a saura da bukatar masu son zuwa, amma gabanin bullar annoba an samu kujerun da su ka yi kwantai don rashin karfin arzikin jama’a ko wadatar abun hannu da ya kara ta’azzara daga rage daukar nauyin lamuran hajji da gwamnatoci su ka yi.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki