Kotu Ta yi Sammacin Emefiele kan badakalar Dala Miliyan 53
Babbar Kotun Abuja ta sammaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a kan ya bayyana gabanta ranar Laraba dangane da shari’ar sama da Dalar Amurka miliyan 53 na kudaden ‘Paris Club’. A wata kara da aka shigar gaban kotun ranar 20 ga watan Oktoban 2022, Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bai wa Emefiele odar ya bayyana a gaban kotun ran 18 ga Janairu don sauraron shari’ar. Umarnin kotun ya biyo bayan karar da lauya Joe Agi, ya shigar ne kan kamfanin Linas International Ltd da Ministar Kudi da CBN ta hannun lauyoyinsa, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi. A cikin karar, yana neman kotu ta bai wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda odar cafke Emefiele da lauyoyinsa tare da gabatar da su ga kotu.K Karar ta taso ne kan hukuncin Dala miliyan 70 da aka yanke wa Linas kan ayyukan lauyoyi game da kudin Paris Club, wanda aka ce Emefiele ya saki Dala miliyan 17 sannan Dala miliyan 53 sun makale. A ranar 23 ga Janairu, 2020 kotu ta yanke hukuncin cewa dole Emefiele ya bayyana “...