Hukumar NAHCON Ta Ce Ya Zuwa Yanzu Kimanin Maniyyata 33,818 Ne Suka Isa Madina Cikin Jirage 80.
Babban Jami’in dake lura da Ofishin hukumar NAHCON na Madina Sheikh Ibrahim Idris Mahmud ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis a ofishin hukumar NAHCON da ke Madina. Ko’odinetan ya ci gaba da cewa, a cikin wannan lokaci, mahajjata suna gudanar da sallolinsu a masallacin Annabi Muhammad (SAW) tare da ziyartan wasu wuraren ibada da na tarihi. Sheikh Mahmud ya kuma ce hukumar NAHCON ta bude babbar cibiyar Karbar magani a ofishin hukumar da wasu kanana guda uku a wuraren kwana na alhazai domin halartar alhazan da ke bukatar kula da lafiya. Jami’in ya yi nuni da cewa NAHCON tana da kwamitocin sa ido da tantance alhazai da suke zagayawa suna sauraron mahajjata tare da mika rahotonsu ga kwamitocin da abin ya shafa domin gudanar da ayyukan da suka dace, ya kara da cewa tana da burin ganin an kula da bukatun alhazai yadda ya kamata. Ya kuma bayyana cewa a kowane gini akwai manaja a kowane gida da ke daukar alhazai kuma ana sanar da su dakinsa da tu...