Wayar salula ce ta haddasa mutuwar sojojin Rasha 89



Rundunar sojin Rasha ta ce, akwai yiwuwar sojojinta sun yi amfani ne da wayoyin salula wadanda suka bai wa takwarorinsu na Ukraine damar gano matsuguninsu har suka kai musu farmakin da ya kashe 89 daga cikinsu.

Sai dai tuni Rashawa suka fara mayar wa da rundunar sojin martani da suka ce, ta fadi haka ne domin wanke kanta daga zargin sakaci.

Hatta masharhanta da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin sun ce, watakila ma adadin sojojin da suka mutun ya zarta 89.

Asarar sojoji 89, ita ce mafi girma da Rasha ta ce ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Ukraine a cikin watan Fabairun bara.

Sojojin na Rasha sun mutu ne sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar musu a Makiivka da ke yankin gabashin Ukraine, inda Rasha ta mamaye.

(RFI)

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki