Bamu kai Karar Shugaban INEC Kotu ba - DSS
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta musanta labarin da ke yawo cewa tana cikin hukumomin tsaron da suka maka Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu a kotu. Kakakin rundunar, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai, inda ya yi karin haske kan umarnin wata Babbar Kotun Abuja na hana hukumomin tsaro ciki har da DSS din kama Yakubu. Boka ya mutu yana lalata da matar fasto Mun gano wadannin macizai a dajin Ecuador —Masana A ranar Laraba ce dai Alkalin Kotun, M. A. Hassan ya ki amincewa da bukatar tsige shugaban INEC din daga mukaminsa, saboda zargin kin bayyana ainihin kadarorin da ya mallaka. Alkalin ya ce kadarorin da Yakubun ya bayyana haka suke, kuma sun yi daidai da tanadin dokokin Najeriya. Hukuncin dai ya biyo bayan karar da Somadina Uzoabaka ta shigar da Babban Lauyan Gwamnatin da Farfesa Yakubu mai lamba FCT/HC/GAR/CV/47/2022 don tilasta wa shugaban hukumar ta INEC sauka daga matsayinsa, har sai an gudanar da binciken wasu ...