Posts

Showing posts with the label Christiano Ronaldo

An sanyawa Jarirai fiye da Dari 700 sunan Pele a Peru

Image
Hukumar Kididdigar Kasar Peru ta bayyana cewar a yayin da duniya ke alhinin rasa Pele, gwarzon dan kwallon kafa na karni, sunansa zai rayu a tsakanin yara fiye da 700 ‘yan kasar da aka haifa a karshen shekarar 2022. Jerin sunayen da jami’an kasar ta Peru suka fitar ya nuna cewar, bayan mutuwarsa gwarzon dan kwallon kafar, an rada wa jarirai 738 da aka yi wa rajista a hukumance sunan ko dai Pele, ko King Pele, ko kuma Edson Arantes ko Edson Arantes do Nascimento, cikakken sunan zakaran kwallon kafa na duniya sau uku. A ranar 29 ga watan Disamba Pele ya mutu yana da shekaru 82 a duniya, wanda kuma aka binne shi a ranar Talata. Iyayen yara a kasar Peru dai sun saba rada wa ‘ya’yansu sunayen fitattun mutane da suke kauna walau a cikin ‘yan wasa ko kuma shugabanni kamar yadda RFI ya ruwaito. Wata kididdiga ta nuna cewar a yanzu haka, sunan Cristiano Ronaldo ne aka fi rada wa yaran kasar, wadanda adadinsu ya kai dubu 31 da 538. Messi kuwa na da takwarori jarirai 371 ne a baya bay

Kungiyoyi da dama sun so daukata amma na yi wa Al-Nassr alkawari - Ronaldo

Image
Cristiano Ronaldo ya ce kungiyoyin kwallon kafa da dama a sassan duniya sun nuna sha’awar daukar sa amma ya yanke shawarar sanya wa Al-Nassr hannu. A lokacin da Al-Nassr ta gabatar da shi a matsayin dan wasanta a gaban dubban magoya bayan kungiyar a ranar Talata, Ronaldo ya bayyana cewa kungiyoyi a nahiyar Turai da Brazil Amurka da Australia da Portugal sun nemi su dauke shi amma ya zabi zuwa Saudiyya. Jaridar Aminiya ta rawaito Ronaldo na cewa “Kamar yadda na fada a baya wannan dama ce a gare ni ba wai a harkar kwallon kafa ba, dama ce da zan sauya tunanin matasa masu tasowa. “Kungiyoyi da dama daga Nahiyar Turai da Brazil da Amurka da Australia da ma Portugal son so dauka ta amma na yi wannan kungiya alkawari. “Na san abin da nake so da wanda ba na so, kuma wannan babban kalubale ne a gare ni na zuwa wannan kasa, ba don komai ba sai don na kara samun ilimi. “Ina son sabon yanayi, kasa don cimma wani buri na daban tare sa Al-Nassr, wannan shi ne dalilin da ya sa na rungumi