Gamsar da Alhazai Shi ne Abun Da Hukumar NAHCON Ta Fi Baiwa Fifiko
An shiga kwana na 12 na jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2023 inda kimanin mahajjata dubu 30 suka shiga birnin Madina lafiya a matakin farko na gudanar da ayyukan. A yayin da Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta fara aikin jigilar jirage na bana, ta tsara shirin jigilar jirage na kwanaki 25 da za a kammala kafin rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Jeddah ranar 22 ga watan Yuni, 2023. A sanarwar da mataimakiyar Daraktar sashen hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda Usara, tace Sakamakon haka, ayyukan jigilar jiragen NAHCON na ci gaba da gudana kamar yadda aka tsara. NAHCON ta himmatu wajen samar da ingantattun hidimomi ga alhazanta a kowane lokaci. Domin tabbatar da cewa alhazai sun samu kulawa ta musammam, an aike da tawagar ma’aikata tun jirgin farko zuwa Saudi Arabiya domin tabbatar da cewa wuraren kwana da na abinci sun gamsu kafin isowar alhazan kasar. Kafin wannan lokacin, Hukumar ta tantance tare da zabo ma...