Posts

Showing posts with the label TRT Hausa

Ma'aikatan BBC Hausa Da Dama, Sun Ajiye Aikinsu

Image
Akalla ‘yan jarida tara na Sashen Hausa na BBC a Najeriya sun yi murabus a cikin wata daya da ya gabata a wani abin da aka bayyana da cewa ba a taba yin irinsa ba a tarihi  Akalla ‘yan jarida tara na Sashen Hausa na BBC a Najeriya sun yi murabus a cikin wata daya da ya gabata a wani abin da aka bayyana a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kafafen yada labarai na duniya. Aminiya ta gano cewa ma’aikatan da abin ya shafa sun hada da manyan ‘yan jarida guda biyu, ’yan jarida uku na kafafen sada zumunta – biyu daga cikinsu manyan ‘yan jarida ne – babban mai ba da rahotannin harsuna biyu na Hausa/English Africa, mai ba da rahotannin kafafen yada labarai da kuma ‘yan jaridar bidiyo guda biyu. An tattaro cewa yayin da biyar daga cikin ‘yan jaridar suka bar watan Disambar da ya gabata; Sauran hudun sun yi murabus ne a ranar Litinin din da ta gabata don shiga sabon sashen Afirka na Rediyo da Talabijin na Turkiyya (TRT) a Istanbul. “Wannan lamari ba a taba ganin ir...