Posts

Showing posts with the label Lafiya

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tantance Lafiya Kafin Aure A Kano

Image
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure. Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka da su ba. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar tana ganin ya zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara masu fama da matsalolin lafiya kamar su sickle cell anemia, HIV/AIDS, da hepatitis. Wannan shiri dai ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga fannin kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadi. Dokar ta wajabta yin gwajin tilas na HIV/AIDS, Hepatitis, genotype, da sauran abubuwan da suka dace kafin aure. Har ila yau, ya haramta duk wani wariya ko kyama ga mutanen ...

Jahar Kano Za Ta Hada Gwiwa Da Canada A Fannonin Bunkasa Lafiya, Ilimi, Noma.

Image
Gwamnatin jihar Kano ta sake bayyana kudurinta na hada gwiwa da kasar Canada a fannonin kiwon lafiya, ilimi, noma, da sauran fannonin ayyukan dan adam domin amfanin bangarorin biyu. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Canada a Najeriya, mai girma James Christoff wanda ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Kano a yau. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi tsokaci kan kyakkyawar alakar da ke tsakanin Kano da gwamnatin Canada a fannonin ilimi, noma, kimiyya da fasaha da dai sauransu. A cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, mai magana da yawun gwamnan ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na da manufar samun moriyar juna, kuma Kano za ta ci gaba da samar da duk wani yanayi da ya dace domin hadin gwiwar yin aiki. Gwamnan ya kuma nemi taimako a fannonin sauyin yanayi, ban ruwa na zamani da sake farfado da shirin bayar da tallafin karatu ga ‘yan asalin Kano da aka yi a farkon shekarun 80s. ...

Yin Waya Fiye Da Minti 30 A Sati Na Kara Hawan Jini —Bincike

Image
Masana kiwon lafiya sun gano cewa yin waya na sama da minti 30 a mako guda na haddasa karuwar cutar hawan jini da kashi 12. Rahoton da Kungiyar Likitocin Zuciya na Nahiyar Turai ta fitar a ranar Juma’a ya bukaci jama’a da su takaita yin waya domin kare lafiyar zukatansu. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rahoton likitocin da aka wallafa a mujallar  Digital Health  yana nuna yin waya na sama da minti 30 a mako na kara barazanar kamuwa da cutar hawan jina da kashi 12 cikin 100. Mujallar, wadda a mayar da hankali a kan yadda na’urorin zamani ke shafar lafiyar zuciya, ta ce hakan bai shafi yawan shekarun da mutun ya yi yana amfani da waya ko sanya waya a lasifika ba. Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Aikin Likita tat Kudancin Guangzhou da ke kasa China, ya kara da cewa masu amfani da waya sun fi mara sa yi yiwuwar kamuwa da hawan jini da kashi 7 cikin 100. Farfesa Qin ya a halin yanzu kusan biliyan 1.3 masu shekaru 30 zuwa 70 na da hawan jini, wadda ke iya kaw...

Fiye da kashi 48 na al'ummar Afrika ba sa samun kulawar lafiya- WHO

Image
  Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ‘yan Afrika miliyan 672 wanda ke wakiltar kashi 48 na al’ummar nahiyar basa samun kulawar lafiyar da ya kamata yayinda suke rayuwa cikin cutuka. WHO ta ce dai dai lokacin da kasashe ke baje hajar gagarumin ci gaban da suka samu a bangaren kiwon lafiya, yayin bikin ranar Lafiya ta Duniya har yanzu Afrika na ganin mummunan koma baya a bangaren. Daraktar hukumar WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta ce bangaren kiwon lafiya na ci gaba da samun koma baya a nahiyar wanda ke da nasaba da rashin kulawar shugabanni don habaka sashen. A sanarwar da ta fitar a ranar lafiya ta Duniya wato World Health Day da ke gudana a kowacce ranar 7 ga watan Aprilu, shugabar ta WHO reshen Afrika, ta ce gazawar bangaren lafiya ya haddasa karuwar cutuka a sassan nahiyar da kuma tsanantar cutuka masu hadari. Dr Matshidiso Moeti ta ce abin takaici yadda hatta kananun cutukan da basu kai su yi kisa ba, su ke iya kashe tarin jama’a a nahiyar ta Afrika saboda gurguncewar b...

Mutane biliyan biyar ka iya kamuwa da bugun zuciya a duniya

Image
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, kimanin mutane biliyan biyar na fuskantar gagarumin hatsarin kamuwa da ciwon zuciya saboda cin abinci mai dauke da kitse da ta bayyana amatsayin guba L A shekarar 2018 ne, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta yi roko da a kawar da cimakar da ke dauke da kitse ganin yadda mutane dubu 500 suka yi mutuwar-farar-daya a sassan duniya sakamakon wannan cimakar. WHO ta ce, kasashen duniya 43 da ke dauke da jumullar mutane biliyan 2 da miliyan 800, sun dauki matakin daina kalace da irin wannan cimakar a kasashensu, amma har yanzu akwai mutanen duniya kimanin biliyan biyar da aka gaza ba su kariya a sassan duniya. WHO ta ce, Masar da Australia da Koriya ta Kudu, na  cikin kasashen duniya da suka yi watsi da gargadinta duk da cewa, su ke kan gaba a jerin kasashen da aka fi samun masu kamuwa da ciwon zuciya skamakon yawan cin abinci mai kitse. Ana yawan cakuda wannan kitsen a cikin cimaka daban-daban da suka hada da man girki da abincin gwangwani da wasu kunsassun k...

Tinubu ba zai ci amanar ’yan Arewa ba, ya dace ya yi mulki – Gwamna Badaru

Image
Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya karyata rade-radin da ake yi na cewa dan takarar Shugaban kasa na APC, Ahmad Bola Tinubu zai yi butulci ga Yan arewa idan ya ci zabe Ya yi ikirarin cewa makusantan dan takarar shugaban kasa sun nuna shi ba maciya amana ba ne. Kuma sun tabbatar da shi a matsayin wanda ba mai kabilanci ba ne kuma mai kishin addini.” Gwamnan jihar Jigawa ya kara da cewa duk abin da Bola Tinubu ya yi a burinsa na zama shugaban kasa, ya yi tare da cikakken masaniyarsa d Ganduje da Nuhu Ribadu, mutanen da suka yi fice wajen kishin kasa. Muhammadu Badaru wanda ya  tuno kan yadda Malamai suka tursasa shi ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a Kudu, ya ce zabin Bola Tinubu an yi shi ne da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar Nijeriya. “Magana game da lafiyar kwakwalwarsa da lafiyarsa, ziyarar da muka yi a Makka kwanan nan a Ummara inda Tinubu ya yi tafiya mai nisa ba tare da shiga mota ba da kuma yadda ya yi dawafi  da Sa'ayi ...

Masu Sukar Lafiyata Ba Su Da Abin Yi Ne —Tinubu

Image
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya ce sukar lafiyarsa da wasu ke yi shirme ne tsagwaronsa. Da yake zantawa da Tashar Freedom Radio ta Kano a Saudiyya, Tinubu ya ce ya yi Dawafi inda ya kewaye Ka’abah sau bakwai ya kuma yi Safa da Marwa wanda mara lafiya ba zai iya aikata hakan ba. Masu sukar Tinubu sun dage da kira kan cewa dan takarar ba zai iya rike Najeriya ba saboda rashin koshin lafiya. Sai dai Yinubun ya ce masu korafi game da lafiyarsa shirme ne kawai, saboda “Yanzu na kammala aikin Umarah, na yi Dawafi sau bakwai da Safa da Marwa da kaina. “Shin wanda ba shi da lafiya zai iya aikata hakan? Don haka wannan tsohon labari ne, masu yayata hakan ba su da abin yi face karya da shirme. “Kwarai ga ni a Saudiyya, bukatar kaina ta kawo ni. Tun fil azal ni mai sha’awar yin Umarah ne saboda dama ce ta ganawa da Ubamgiji,” in ji Tinubu. Game da batun halartar tarurrukar tattaunawa da jama’a, Tinubu ya ce masu korafin ba a ganin shi a wajen tarurrukan wadanda s...