Dawo Da Makarantar Koyar Da Sana'ar Fim Dake Tiga, Babbar Nasara Ce Ga Masana'antar Kannywood- Abba El-Mustapha
Shugaban Hukumar tace Fina-finai da Dab'i ta Jahar Kano, Abba El-mustapha ya bayyana farin cikinsa tare da karfin gwiwa dangane da kara bude makarantar koya Sana'ar Fina-finai dake garin Tiga a Jahar Kano. A sanarwar da jami'in hulda da jama'a na Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu, tace nada sabon Daraktan Makarantar Alh. Dr. Maigari Indabawa yace, hakika abu ne da ya dace duba da yadda Sana'ar fina-finan ke bukatar sauyi ta fannin ilimi Wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin Kano tare da kawo kudin shiga. Ya Kara da cewa, da yawa daga cikin yan masana'antar na bukatar Samin karin horo domin a nuna musu sabbin da baru ta yadda Sana'ar zata tafi da zamani haka kuma su kansu yan masana'antar zasuyi gogayya da takwarorin su na kasashen waje . Abba El-mustapha ya godewa Gwamna tare da yiwa sabon shugaban makarantar fatan alheri tare da addu'ar Allah yasa yafara a sa'a ya Kuma gama lafiya. El-mustapha ya kuma yi wa saur...