Abun Da Tinibu Da Kwankwaso Suka Tattauna A Kasar Waje
Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa. Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje. A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karbi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa hudu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na kasar Faransa. Majiyarmu ta ce a yayin ganawar, Tinubu ya bukaci hadin kai domin aiki tare da Sanata Kwankwaso — wanda ya lashe kuri’un Jihar Kano a zaben 2023. Kwankwaso da shugaban kasar da ke jiran rantsarwa nan da mako biyu masu zuwa sun kuma amince za su ci gaba da tattaunawa kan wannan batu. Majiyar ta ce mai dakin Kwankwaso da zababben Sanata Abdulmumini na Jam’iyyar NNPP ne suka raka madugun Kwankwasiyya zuwa wurin ganawar. A bangaren Tinubu kuma, matarsa, Sanata Oluremi da Mataimakin...