Posts

Showing posts with the label Tallafin Karatu

Matukin Adaidaita Sahu Dan Kano Da Ya Tsinci Kudi Ya Mayar, Ya Samu Tallafin Miliyan 250 Don Yin Karatu

Image
A wani abin da ya yi kama da gasa, matashin nan mai tuka Adaidaita Sahu mai shekaru 23 a Kano, Auwalu Salisu, wanda ya tsinci kudin wani dan kasuwa dan kasar Chadi har naira Miliyan 15  da ya manta su a kekensa tun a 2023, an ba shi tallafin karatu na naira Miliyan 250 har zuwa matakin karatun digiri na uku  KANO FOCUS ta ruwaito cewa, LEADERSHIP Media Group ta yi bikin karamar  Auwalu a ranar Talata a wajen taron shekara-shekara da kuma bikin karramawa a matsayin wanda ya lashe lambar yabo ta ‘Fitaccen matashin matashin shekarar 2023’, saboda nuna gaskiya da ya yi. Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, wanda aka karrama shi a matsayin Gwarzon dan siyasar LEADERSHIP na shekarar 2023, shi ne ya fara ba Awwalu guraben karatu a Jami’ar Baze da ke Abuja har zuwa matakin digirin digirgir. Bayan haka, gwamnan jihar Neja, kuma wanda ya lashe kyautar Gwarzon Gwamnan na LEADERSHIP, Mohammed Umar Bago, ya mayar da martani cikin raha yana ma...