Ayyukan Da Zan Yi Wa Al'umar Mazabata Cikin Shekarar 2024 - Abdulmumin Jibrin Kofa
Bayan rantsar da ni a matsayin ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji, na yi hoɓɓasar ganin na kawo ayyukan raya ƙasa da ci gaban yankina. Kamar yadda buƙatun ainihin aikin da aka zaɓe ni don shi suke, na duƙufa ba dare ba rana wajen yin bincike domin gabatar da ƙudurorin da zan gabatar a zauren majalisa a ’yan watanni masu zuwa, waɗanda za su amfani ’yan mazaɓata da ma ƙasa baki ɗaya. A sakamakon haka, na tattauna da shugabannin kwamitoci daban-daban a Majalisa, na kuma rubuta wasiƙun neman ayyuka masu yawa da za aiwatar a mazaɓata a 2024, ƙari a kan wasu da zan yi da aljuhuna, kamar yadda na saba yi a baya. Yana da muhimmanci a fahimci cewa idan ban da aikin tituna (waɗanda na saka a kasafin kudin 2016, amma ba a aiwatar da su ba), na kawo ayyukan raya kasa masu tarin yawa a mazaɓata, na samar da gurabun ayyukan yi ga mutanen mazaɓata a hukumomi da ma’aikatun gwamnati masu yawa da kuma wasu hukumomin tsaro, duk waɗannan za a iya zuwa a tantance su. Du...