Search This Blog

Showing posts with label Kudin makaranta. Show all posts
Showing posts with label Kudin makaranta. Show all posts

Tuesday, 29 August 2023

Sanatan Kano Ya Ba Dalibai 620 Tallafin Karatu A BUK

 


Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin ya ba wa daliban mazabarsa 628 tallafin karatu a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Aminiya ta gano cewa duk dalibin mazabar da ya rabauta ya samu tallafin N50,000 daga dan majalisar.

Da yake bude rabon tallafin, shugaban ma’aikatan Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya ce dan majalisar ya yi haka ne domin ba wa daliban mazabarsa damar neman ilimi a manyan makarantu.

Kakakin Mataimakin Shugaban Majalisar, Ismail Mudashir, ya ce daliban mazabar Kano ta Arewa da ke sauran manyan makarantu a fadin Najeriya ma za su amfana da tallafin.

Don haka ya bukaci daliban da suka amfana da su yi amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ta dace sanna su kara jajircewa wajen neman ilimi.Wani dalibin aji hudu a jami’a da ya samu tallafin, Adama Iliyasu Rabiu, ya yaba wa dan dan majalisar tare da rokon Allah Ya saka masa.

(AMINIYA)


Monday, 28 August 2023

Yanzu-Yanzu : Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Rage Kashi Hamsin Cikin Dari Na Kudin Da Daliban Manyan Makarantu Ke Biya

Gwamna Abba Kabir ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Litinin

Gwamnan yace ya bawa Shugabannin makarantun gaba da Sakandire dake Kano umarnin rage kudin da dalibai ke biya daga kaso dari zuwa kaso hamsin

Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook, ya ce wannan mataki ya faru ne sakamakon tsananin rayuwa da jama’a ke fuskanta a halin yanzu a kasar nan 


Thursday, 24 August 2023

Gwamnan Kano Zai Biya Wa Daliban BUK 7,000 Kudin Makaranta

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa daliban da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta.

Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Laraba.


“Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biya wa ɗaliban jihar Kano da ke karatu a BUK su kimanin dubu bakwai kuɗin makaranta,” kamar yadda ya wallafa.

Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi.


A sakamakon karin, dalibai da dama sun rika neman gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa musu.

Hatta jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita wa’adin lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda tsadar.

(AMINIYA)

Saturday, 7 January 2023

Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta - Kungiyar Dalibai

Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ''gaggawar sa baki'' game da ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'in ƙasar ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar''.

Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ''duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari'',

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami'o'in ƙasar suka bayyana ƙarin kuɗin makaranta.

To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama.

Dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya.

Wasu jami'o'in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu.

dalibai
othersCopyright: others
To sai dai ƙungiyar ta ce kundin tarin mulki ya wajabta wa gwamnati samar da ingantaccen ilimi ga 'yan ƙasa, don haka dole ta samar da kuɗin gudanar da ɓangaren ilimi.

Haka kuma Sakataren na NANS ya ce ''matuƙar ba a soke ƙarin kuɗin makarantar da aka yi ba, to kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na ɗaliban ƙasar ba za su koma makaranta ba, saboda ba za su iya biyan wannan kuɗi ba''.

Abin da kuma a cewarsa zai ƙara yawaitar masu aikata miyagun laifuka a fadin ƙasar saboda rashin makoma da ɗaliban ke da shi.

Mista Kankia ya kuma yi gargaɗin cewar ''matukar buƙatarmu ba ta biya ba, to za mu gudanar da gagarumar zanga-zangar da za ta shafi abubuwa da dama a faɗin kasar nan''.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

SAPZ Kano partners ABCOAD to organize FFS Training for Youth and Women.

The Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ) Programme, Kano State, in collaboration with Audu Bako College of Agricultur...