Hajj 2023: Kashi Na Farko Na Alhazan Kano Sun Bar Makkah Zuwa Jiddah Domin Dawowa Najeriya
A ranar Asabar da ta gabata ne rukunin farko na alhazan Kano da suka yi aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya, suka tashi daga Makka zuwa Najeriya. A sanarwar da da Jagoran tawagar 'yan jaridu na aikin Hajji na Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce alhazan sun tashi daga Makka zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz, Jeddah, da misalin karfe goma na safe agogon Saudiyya. Ana sa ran jirgin nasu zai tashi da yamma a wannan rana. Tun a daren Juma’a ne dai aka fara gudanar da tafiyarsu tare da tantance jakunansu na hannu domin tabbatar da aiki da tsarin hukumar alhazai ta kasa. A safiyar ranar Asabar alhazan tare da jakunkunansu sun taru domin shiga manyan motocin bas na alfarma zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz na Jeddah. Wasu daga cikin mahajjatan da aka zanta da su, Zubairu Hudu Sani daga Doguwa, Sirajo Hudu daga Tudunwada, Maryam Abdullahi Garun Malam da Hadiza Hamisu daga kananan hukumomin Bebeji sun gode wa Allah da ya ba su damar yin aikin h