Kwamitin Binciken Kwato Kadarorin Gwamnati nlNa Jihar Kano Zai Gudanar Da Zama Ranar Litinin Mai Zuwa
Kwamitin shari’a na binciken kadarorin gwamnati da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kafa domin binciken gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shirya gudanar da zamansa na farko a ranar Litinin 29 ga Afrilu, 2024. Sakataren kwamitin Salisu Mustapha ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aikewa mai magana da yawun Gwamnan Kano a ranar Asabar. Mustapha ya bayyana cewa zaman zai gudana ne a babbar kotu mai lamba 3 dake cikin sakatariyar Audu Bako a ranar Litinin 29 ga Afrilu, 2024 da karfe 10 na safe. A farkon wannan watan ne Gwamna Yusuf ya kaddamar da wasu kwamitocin bincike na shari’a guda biyu (JCI) domin binciken almubazzaranci da dukiyar jama’a da tashe-tashen hankulan siyasa da kuma bacewar mutanen da suka yi a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023. A yayin kaddamar da mambobin kwamitin, Gwamna Yusuf ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi, inda ya jaddada kudirinsa na bankado tare da gurfanar da wadanda suka ...