Duk wanda ba shi da kuri'a ba zai yi zabe ba - INEC


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jaddada cewa babu wanda zai kada kuri'a a zaben 2023 mai zuwa sai mai katin zabe 

Jami'in zabe na karamar hukumar Gwarzo Mal.Bello Ismail ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki a ofishinsa. 

Bello Ismail ya kara da cewa an samar da sabbin rumfuna saba'in da uku domin rage cinkoso da masu kada kuri'a sama da dubu daya a Gwarzo,Getso,Kutama,Lakwaya,Mada da ,Unguwar tudu dake karamar hukumar Gwarzo.

 Jami’in zaben ya kuma kara da cewa INEC za ta kai unguwanni goma na kananan hukumomin domin rabon kaya daga ranar 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Janairu.

Da yake jawabi a wajen taron sakataren jam’iyyar A.P.C. Samaila Abdullahi ya shawarci hukumar zabe da ta kaucewa tarin pVC na uku.

A nasu jawabin jami'in 'yan sanda DSS, da Civil Defence kira suka yi INEC da su bayar da motocin daukar kayan zabe da jami’ai domin kaisu wuraren da ya dace. 

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da wakilan babban limami, hakimin gundumar, shugabannin jam'iyya da dai sauransu.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki