Gamu Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 4- Dr Dukawa
HALIN DA TITUNAN NAJERIYA SUKE CIKI Tafiyar da muka yi daga Kano zuwa Yola ta dauke mu kimanin awa tara (9.30 na safe – 6.30 na yamma). Kuma na yaba da tukin direbanmu, wani matashi mai suna Uzairu dan kimanin shekara 25/6. Wannan tafiyar ta tuna min da wani majigi da shahararren masanin kimiyar siyasa, Farfesa Ali Mazrui, ya yi a shekarun 1980. Ali Mazrui dan asalin Kenya ne, ya auri ‘yar Najeriya, sun rayu a America har rasuwarsa. Guda daga cikin hanyoyin da Ali Mazrui ya bi wajen nuna tazarar da take tsaknin manyan kasashe da masu tasowa shine yadda ya dauko hoton wani titi a wata babbar kasa (watakil America) da motoci suna gudu kowacce a layinta. Sai ya ce: “duk wanda ka gani yana tuki yana kwane-kwane anan, to a cikin maye yake”. Sai kuma ya dauko wani titi na wata kasar mai tasowa (watakila Kenya ko Najeriya), da motoci suna ta kwane-kwane suna kaucewa ramukan kan titi. Sai ya ce: “anan kuma, duk wanda ka gani yana tafiya sambel babu kwane-kwane to a buge yake!”...