Search This Blog

Showing posts with label Kadarorin gwamnati. Show all posts
Showing posts with label Kadarorin gwamnati. Show all posts

Sunday, 28 April 2024

Kwamitin Binciken Kwato Kadarorin Gwamnati nlNa Jihar Kano Zai Gudanar Da Zama Ranar Litinin Mai Zuwa

Kwamitin shari’a na binciken kadarorin gwamnati da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kafa domin binciken gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shirya gudanar da zamansa na farko a ranar Litinin 29 ga Afrilu, 2024.

Sakataren kwamitin Salisu Mustapha ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aikewa mai magana da yawun Gwamnan Kano a ranar Asabar.

Mustapha ya bayyana cewa zaman zai gudana ne a babbar kotu mai lamba 3 dake cikin sakatariyar Audu Bako a ranar Litinin 29 ga Afrilu, 2024 da karfe 10 na safe.

A farkon wannan watan ne Gwamna Yusuf ya kaddamar da wasu kwamitocin bincike na shari’a guda biyu (JCI) domin binciken almubazzaranci da dukiyar jama’a da tashe-tashen hankulan siyasa da kuma bacewar mutanen da suka yi a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

A yayin kaddamar da mambobin kwamitin, Gwamna Yusuf ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi, inda ya jaddada kudirinsa na bankado tare da gurfanar da wadanda suka haddasa tashe-tashen hankulan siyasa a jihar kafin da lokacin zabukan da suka gabata.

Gwamnan ya bukaci kwamitin da suyi cikakken bincike a kan almubazzaranci da dukiyar al’umma da aka yi a zamanin gwamnatin da ta shude.

Ya kuma umurci mambobin kwamitin da su kiyaye mutuncinsu, su ci gaba da bin rantsuwar da suka yi, su kuma yi wa al’ummar jihar Kano hidima ta hanyar tabbatar da adalci. Gwamna Yusuf ya fayyace cewa shirin ba wai siyasa ce ko wani mutum aka yi ba, illa dai mayar da martani ne ga al’ummar jihar Kano.

Za ku iya tunawa dai an zabo alkalan manyan kotunan jihar Farouq Lawan Adamu da Zuwaira Yusuf da wasu fitattun mutane aka nada su a matsayin shugabanni da mambobin kwamitocin bincike guda biyu.

Thursday, 18 May 2023

El-Rufai Zai Rushe Kamfanoni 9 Mallakar Makarfi

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya soke lasisin mallakar kamfanoni tara na tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi.

An kuma shirya rushe kamfanoni tara mallakar tsohon gwamnan Jihar.

Aminiya ta fahimci cewa an kai sanarwar janye  hakkin mallaka ga jami’an kamfanonin da abin ya shafa.

Sanarwar ta fito ne daga Daraktan kamfanin rake da ke lamba 11 a Murtala Square, Alhaji Ibrahim Makarfi wanda ya mayar da martani da cewa, “lauyoyinmu za su mayar da martani kan kwace hakkin mallakar kamfanonin”.

Sai dai da yake mayar da martani kan soke hakkin mallakar a wani sakon da ya aike wa Sanata Makarfi, ya tabbatar da samun wasikun soke kamfanonin har guda tara.

Ya ce, “Akwai babban batu. Muna bukatar ganawa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya kotu don dakatar da gwamnatin jiha; kawai sun aiko mana da takardun soke mallaka guda tara”.

Daga cikin kadarorin da abin ya shafa sun hada da filaye guda biyar a Mogadishu, filaye uku a kan titin Kwato, da fili daya a Doka.

A cikin takardun soke hakkin mallakar da magatakardar hukumar kula da bayanan kasa ta Kaduna (KADGIS) ya sanya wa hannu, Mahmud Aminu ya ce, “An umarce ni da na sanar da ku cewa mai girma Gwamnan Jihar Kaduna a cikin ikon da aka ba shi a karkashin sashe na 28 (5) (a) da (b) na dokar amfani da filaye ta 1978, ya kwace hakkin mallakar wadannan kadarori da aka ambata”.

AMINIYA 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...