Posts

Showing posts with the label Madaki

Nan Gaba Kadan Za A Gurfanar Da Ali Madaki A Kotu

Image
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa cikin kankanin lokaci za ta gurfanar da zababben Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Dala a karkarshin tutar Jam’iyar NNPP, Honorabil Aliyu Madaki. Dan Majalisar dai ya shafe kawamaki biyu a hannun ’yan sanda kamar yadda kakakin rundunar ’yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatarwa Aminiya. Atiku zai garzaya kotu kan zaben shugaban kasa Yau Kotun Koli za ta ci gaba da shari’ar sauyin kudi Ana dai zargin Honorabul Aliyu Madaki da laifin fito da makami a fili wanda zai iya zama barazanar ga zaman lafiyar al’ummar jihar. An tsare Aliyu Madaki ne washegarin da rundunar ta cafke Shugaban Masu Rinjaye na Majaslisar Tarayya, Honorabul Alhassan Ado Doguwa. ’Yan sanda sun cafek Doguwa ne kan zargin tayar da zaune tsaye da kuma harin da aka kai Ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Karamar Hukumar Tudunwada ta Jihar Kano a lokacin da ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na Majalisar Tarayya. Ana kuma al...