Posts

Showing posts with the label London

Yadda jami'an tsaro suka tsare Peter Obi a London

Image
  Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP ya ce jami’ai sun tsare tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi a birnin London. Mai magana da yawun kwamitin kamfe na jam’iyyar LP, Diran Onifade ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a filin jirgin sama na Heathrow da ke London. Ta ƙara da cewa jami’an shige da fice na Birtaniya ɗin ne suka titsiye tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar. Diran Onafide ya ce hukumomi a Birtaniya sun tsare tare da yin tambayoyi ga tsohon gwamnan na jihar Anambra kan wani lamari da ya shafi wani mutum da ke yin sojan-gona da suna Peter Obi. Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an sun sassauta wa Petetr Obi ne bayan wasu ƴan Najeriya da ke a filin jirgin sun sanya baki. Peter Obi dai ya isa birnin na London ne domin bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista. Bayanin ya nuna cewa bayan saukar Peter Obi a filin jirgin na Heathrow da ke London, jami’an tsaro sun zo wuri