Posts

Showing posts with the label Saudiyya

Yakin Sudan: Sojoji Da ’Yan Tawaye Za Su Koma Teburin Sulhu A Saudiyya

Image
Sojoji da mayakan RSF da ke yakar juna a Sudan za su koma kan teburin sulhu ranar Lahadi bayan sun kwana suna ba-ta-kashi a Khartoum, babban birnin kasar. Wani babban jami’in gwamnatin Sudan ya ce za su koma tattaunawar ne bayan barkewar yaki tsakaninsu duk da yarjejeniyar da suka sanya hannu na kare fararen hula da ayyukan jin kai. Jami’in ya bayyana cewa kasar Saudiyya mai masaukin baki ta gayyaci Babban Hafsan Sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan zuwa babban taron kasashen Larabawa da zai gudana a birnin Jidda ranar Juma’a. Sai dai wasu jakadun kasashen Larabawa sun bayyana cewa ba a tsammanin zuwan Janar Burhan zai halarci taron ba saboda dalilan tsaro. An gayyaci Janar Burhan ne a matsayinsa na shugaban kwamitin rikon kasar, wanda aka dora wa alhakin tsara yadda za a mika mulki ga zababbiyar gwamnati anan gaba, Abokin hamayyarsa kuma shugaban mayakan RSFk, Janar Mohamed Hamdan Dagalo kuma shi ne mataimakinsa a kwamitin. Wani jakadan kasar Saudiyya ya bayyana cewa kawo yanzu d...

Saudiyya Ta Yi Wa Messi Tayin Ninkin Albashin Ronaldo

Image
  Kungiyoyin kwallon kafa a kasar Saudiyya na zawarcin gwarzon dan wasan duniya, Lionel Messi, na kungiyar PSG, da tayin albashin da ya zarce na kowane dan wasa a duniya. Rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke zawarcin Messi a Saudiyya ta yi masa tayin albashin Naira biliyan 183.5 (Dala miliyan 400) a shekara, idan kwantaraginsa ya kare da PSG a wata mai zuwa. Kafar labarai ta Telegraph ta kasar Birtaniya ta ce dan wasan ya fara tunanin duba tayin kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da Kyaftin din na kasar Argentina kan kwangilar da take masa tayi, bayan dakatarwar da PSG ta yi masa. Idan hakan ta tabbata, Messi zai rika karbar kusan ninki biyun albashin babban abokin hamayarsa Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu Al Nassr ta kasar Saudiyya ke biyan sa Naira biliyan 96.3 Dala miliyan 210 a shekara, zuwa 2025. A halin yanzu dai, Cristiano Ronaldo ne dan wasa mafi albashi a duniya, inda Messi ke biye da shi, kafin Kylian Mbappe na Farasan da PSG. Wannan sabuwar ta taso ne bay...

Saudiyya Ta Kwashe ’Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan Zuwa Kasarta

Image
Gwamnatin kasar Saudiyya ta kwashe wasu daga cikin ’yan Najeriya da suka makale a yakin da ya barke a Sudan zuwa kasarta. Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya, Zubairu Dada, ya ce Saudiyya ta tura jiragen ruwa da suka kwashe ’yan Najeriya zuwa birnin Jeddah na kasarta, bayan barkewar yaki a Sudan. Ma’aikatar ta ce daga bisani za a maido da ’yan Najeriyan da aka kai Saudiyya gida, kuma gwamnatin Tarayya na kokarin ganin cewa babu dan Najeriya ko daya da ya rage a Sudan kafin cikar wa’adin awa 72 da bangarorin da ke yaki da juna suka bayar na tsagaita wuta. Ta bayyana cewa a kokarinta na kwashe ’yan Najeriya da suka makale bayan barkewar yakin, Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira miliya 552 kan daukar hayar motocin da za su fitar da su zuwa iyakar Sudan da kasar Masar. Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyema, ya ce an dauki hayar bas-bas 40 da za su kwashi ’yan Najeriya daga Khartoum, babban birnin Sudan zuwa iyakar kasar Masar da ke Aswan, inda za su hau jirgi zuwa gi...

Labari Da Dumiduminsa: An Wa Watan Sallah A Saudiyya

Image
  Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023. An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana, hakan na nufin Saudiyya ta kammala azumin Ramadan 29. Gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

Najeriya Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Da Saudiyya

Image
  Najeriya ta samu nasarar yin taro da hukumomin aikin hajji na Saudiyya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin bana.   Karamin ministan wajen Najeriya Ambasada Zubairu Dada ne ya jagoranci tawagar Najeriya wajen kulla wannan yarjejeniya da ke zama ka’idar amincewa kowace kasa ta kawo alhazai. Rattaba hannu kan yarjejeniyar ya biyo bayan wata ganawa ta yanar gizo tsakanin shugaban hukumar Alhazan Zikrullah Kunle Hassan da hukumomin aikin hajji na Saudiyya a watan Disambar bara. Kwamishinan ma’aikata da tsara manufofi na hukumar Alhazan Nura Hassan Yakasai wanda ke cikin tawagar ya bayyana cewa Saudiyya ta amince da dawowa da Najeriya yawan kujeru na asali da ta ke samu mutum dubu 95. Hakanan Yakasai ya ce a yanzu ba dogon bincike kan cutar korona bairos matukar maniyyaci ya na da shaidar gwajin cutar. Malamai sun shiga fadakar da maniyyata don kara fahimtar dokokin aikin da zummar samun ladan wankuwa daga zanubai. Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala L...

Mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022- Saudia

Image
Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta ce kimanin mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa wannan adadin a cewar ma’aikatar ya hada da baki su miliyan hudun da suka samu izinin shiga kasar domin Hajjin Umarah. Kamfanin dillancin labarai na SPA ya rawaito a ranar Alhamis cewar, Ma’aikatar ta yi amfani da harsuna 14 wajen isar da muhiman bayanai da suka shafi addini da kiwon lafiya da sauransu ga maniyyatan yayin zamansu a kasar. Kazalika, ta ce ta tabbatar da maniyyatan sun samu kulawar da ta dace wajen gudanar da harkokinsu da suka hada yanka da ziyartar wurare da sauransu. Ta kara da cewa, ta sahale wa masu rike da biza daban-daban ibadar Umarah a wannan shekarar. Ta ce a 2022 ne ta kyale masu bizar yawon shakatawa suka yi Umarah yayin zamansu a kasar, wanda hakan shi ne karon farko da irin hakan ta faru.