INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe A Enugu, Kano, Akwa Ibom Sakamakon Rikici, Sace Jami'an Zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da sake gudanar da zabukan da aka gudanar a wasu mazabu na jihohin Enugu, Kano, da Akwa Ibom, sakamakon tarzoma, da rashin bin ka’ida, da kuma sace jami’an zabe. Yankunan da abin ya shafa sun hada da mazabar Enugu ta Kudu 1 a jihar Enugu, da kuma mazabar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, da kuma mazabar Kunchi/Tsanyawa dake jihar Kano. Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sam Olumekun, kwamishinan na kasa & shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, a ranar Asabar. Dakatarwar ta biyo bayan rahotannin ‘yan daba da sace kayan zabe a wadannan jihohin. A mazabar Enugu ta Kudu 1, an dakatar da zabukan a dukkan runfunan zabe takwas da aka yi na farko A mazabar Kunchi da Tsanyawa da ke jihar Kano, an dakatar da zabuka a dukkanin mazabu goma da ke karamar hukumar Kunchi sakamakon mamayewa da barna da kuma kawo cikas da ‘yan daba. An yanke wannan hukuncin ne bisa ga sashe