Tsadar Kayan Abinci: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kano Za Ta Fara Kama Dukkanin Wadanda Ta Samu Suna Boye Kayan Abinci
Shugaban Hukumar, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a ofishinsa Muhuyi Magaji ya ce " ..a dokar jahar Kano, boye kayan abinci haramun ne" don haka zamu dauki matakin da ya dace kan masu aikata hakan. Shugaban Hukumar ya ci gaba da cewa duk da cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gudanar da zama na musammam tare da manyan 'yan kasuwa, Amma yace hakan na zai hana ofishinsa nasa yin abun da ya dace ba, kasancewar daman hukumar na karkashin Ofishin Gwamnan ne. "Mun yi wani aiki a baya wanda al'uma suka ji dadin shi, don haka mun karbi kiraye - kiraye ta hanyoyin sadarwa, wasu sun tako kafa da kafa su kira su ce wai abubuwan da muka yi a baya me yasa yanzu ba ma yi, to shi ne na ja hankali cewa kowanne abu ya na zuwa ne da nasa matsalar, wancan lokacin matsalar ta faru ne lokacin zaman gida sanadiyyar cutar Coronation.." Batista Muhuyi ya kara da cewa wancan yanayi ya haifar