Posts

Showing posts with the label Baya Da Kura

Da Sanin Ganduje Tinubu Ya Gana Da Kwankwaso —Kofa

Image
  Zababben dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje yana da masaniya game da ganawar da shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu ya yi da Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa. Aminiya  ta ruwaito yadda Tinubu da Kwankwaso suka yi ganawar sama da sa’o’i hudu a ranar Litinin. A wani sautin waya da aka nada, an ji Ganduje yana bayyana rashin jin dadinsa kan ganawar Tinubu da Kwankwaso, inda ya ce ya yi hakan ne a kashin kansa. An jiyo shi yana cewa ya kamata Tinubu ya tuntube shi ko kuma ya gayyace shi taron da ya yi da Kwankwaso. Sai dai a zantawarsa da Aminiya, Kofa, wanda ya halarci ganawar da shugabannin biyu suka yi a Faransa, ya ce Ganduje ya tabbatar masa da cewa Tinubu ya tuntube shi kafin a yi taron. “Na yi matukar kaduwa da na saurari sautin, amma ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne ina son tabbatar muku cewa an tuntubi Gwamna Ganduje. “Kuma shi da kansa ya tabbatar min cewa zababben shugaban kasar ya gayyace shi, ya kuma shaida m...