Posts

Showing posts with the label Farfesa Abdullahi Saleh

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Bayyana Cigaban Da Ya Samar Cikin Kwanaki 100, Ya Bukaci Maniyyata Su Ba Da Hadin Kai – Daga Nura Ahmad Dakata

Image
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana muhimman nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancinsa a cikin kwanaki 100 na farkon jagorancinsa   A wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu a Kano Farfesa Sale Usman, ya jaddada muhimmancin koyi da shugabancin da ya gabata, inda ya ce, “A rayuwa duk wanda ya riga ka mulki, ko ya yi kura-kurai, ko ya yi nasara, sai ka yi addu’a Allah ya karba nasa ayyukan alheri kuma ya gafarta masa kurakuransa. Muna yin iya kokarinmu a yanzu kuma muna addu’ar Allah Ya taimakemu mu ci gaba da tafiya kan hanya madaidaiciya”.   Ya kuma bayyana cewa shugabancinsa yana daukar darasi daga ayyukan magabata, da amfani da nasarorin da suka samu da kuma gujewa kura-kuransu.   Da yake yin tsokaci kan hakan, ya ce, “A cikin kwanaki 100 da muka yi muna shugabanci, mun cimma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama na rage farashin tikitin jirgin sama idan aka kwatanta da wanda aka biya a bara. ...