Posts

Showing posts with the label Sabbabbin Kudi

Da dumi-dumi: CBN ta kara wa’adin karbar tsofaffin kuɗin

Image
  A karshe dai babban bankin Najeriya CBN ya kara wa’adin daina karɓar tsofaffin kudi har zuwa nan da kwanaki 10.   Majiyarmu ta rawaito a wata sanarwa da gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sabon wa’adin zai kare ne 10 ga watan Fabrairun 2023. Duk da haka, har yanzu ’yan Najeriya za su iya mika tsofaffin takardun Kudinsu kai tsaye zuwa bankin CBN har nan da ranar 17 ga Fabrairu, 2023.   Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil ‘Yan Najeriya dai sun yi ta kokawa kan rashin wadatattun sabbin kudin wanda da farko aka ce wa’adin zai kare a ranar 31 ga watan Janairu . A baya dai CBN ta ce ba za ta kara wa’adin ba.  

Take-Taken Da Ake Nufi Da Karancin Mai Da Sauya Fasalin Naira —Tinub

Image
Dan takarar Shugaban Kasa karkashin Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi zargin matsalar karancin mai da ake fuskanta da sauya fasalin wasu takardun Naira da aka yi, take-taken neman wargaza Zaben 2023 ne kawai. Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yakin neman zaben APC da ya gudana ranar Laraba a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Na tafka kuskure a tafiyar Buhari, ba zan maimaita da Tinubu ba — Naja’atu Muna da hujjoji kan cewa Tinubu tsohon mai laifi ne – Dino Melaye  “Ba sa son zaben ya gudana. So suke su wargaza shi. Za ku bari hakan ta faru?, in ji Tinubu. Dan takarar ya ce yana da yakinin matsalar karancin fetur ba za ta hana ’yan Najeriya zuwa kada kuri’a ba ranar zabe. “Sun fara bullo da batun ‘babu mai, kar ku damu, idan babu mai za mu taka da kafa zuwa wajen zabe. “Idan kun ga dama ku kara kudin mai, ko boye man ko kuma ku canza wa naira launi, za mu ci zabe,” in ji shi.