Hajj 2014 : Hukumar NAHCON Ta Kafa Kwamitin Bitar Ka'idojin Samar Da Abinci Da Gidaje.
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazari kan wasu sharuddan da suka shafi masauki da abinci don samar da ingantacciyar hidima a lokacin aikin Hajjin 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na Hukumar Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi a wurin taron, mai rikon Shugabancin Hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi OON, fwc, ya bayyana cewa sake duba ka’idojin da ake da su za su taimaka wajen inganta ayyukan masu ba da hidima wanda hakan zai amfanar da Alhazan Najeriya. A cewarsa, kundin tsarin gudanarwar kwamitin ba sabon sabon abu ba ne, amma wata hanya ce kawai ta yin la'akari da tsarin da ake da shi don samar da kyakkyawan sakamako. “Abin da muke yi yanzu ba wai sabon abu ba ne kawai don inganta yadda muke yin abubuwa. Kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na duniya, muna bukatar mu kasance da Æ™wazo. Kamar yadda al'ada ce ta duniya, dole ne mu inganta ta hanyoyinmu, don dacewa da mafi kyaw...