Search This Blog

Showing posts with label Fasinjoji. Show all posts
Showing posts with label Fasinjoji. Show all posts

Tuesday, 10 January 2023

Maharan Jirgin Edo Na Neman Fansar N520m

Yan bindigar da suka sace fasinjoji a Tashar Jirgin kasa ta Ekehen da ke Jihar Edo na neman Naira miliyan 520 a matsayin kudin fansa.

Rahotanni sun ce maharan sun kira iyalan fasinjoji 26 da ke hannunsu, suka yanka musu fansar Naira miliyan 20 a kan duk mutum daya.

Zan dora daga inda El-Rufai ya tsaya a Kaduna —Uba Sani
Kano 2023: Dalilin ba wa Gawuna takarar Gwamna —Ganduje
Wani shugaban matasa a yankin, Benson Ordia, da ya tabbatar da hakan, ya ce gwamnatin jihar ta ce za ta gudanar da bincike na tsanaki a yankin.

Sai dai kakakin ’yan sandan jihar, Chidi Nwanbuzor, ya ce ba shi da masaniya kan kudin fansar da maharan suka yanke kan fasinjojin.


A ranar Asabar ce maharan suka kai hari tare da yin awon gaba da fasinjoji akalla 32 a tashar jirgin kasan.

Sai dai jami’an tsaro sun ceto mutum shida daga cikin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, wadanda uku daga cikinsu kananan yara ne.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ’yan bindiga ke kai wa jirgin kasa hari tare da sace fasinjoji, bayan wani hari da suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022

Sunday, 8 January 2023

Labari da dumiduminsa : 'Yan bindiga sun sake yin garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa

Watanni bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kuma kai farmaki tashar jirgin kasa tare da kwashe mutane da yawa a Jihar Edo dake kudu maso kudancin Najeriya.

Fasinjojin da suka samu raunuka, an ce suna jiran su hau jirgin kasa a wurin da lamarin ya faru, kafin su nufi garin Warri mai arzikin man fetur.

Tuni dai hukumar 'yan sanda ta Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a cewar tashar talabijin ta TVC.

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai farmaki tashar jirgin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar 7 ga watan Janairu, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su fito da shirinsu. 

A ranar 28 ga Maris, 2022 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. 2022 .

Har yanzu dai Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ba ta ce uffan ba game da sabon ci gaban da aka samu a daidai lokacin da ake hada wannan rahoto.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...