Angola Ta Zarce Najeriya A Hako Danyen Man Fetur —OPEC
Adadin danyen man da Najeriya ke hakowa ya ragu zuwa ganga dubu dari 9 da 99 a kowace rana a watan Afrilu. Wannan lamarin dai ya sa yanzu Angola ta shiga gaban Najeriya saboda tana samar da ganga miliyan 1 da 63 a kowace rana. Dalilai 8 da ke tunkuda mutane zuwa É—abi’ar LuwaÉ—i da MaÉ—igo An kammala kwaso ’yan Najeriya da suka makale a Sudan —NIDCOM Wannan na kunshe ne a cikin rahoton wata wata na watan Afrilu da kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai ta fitar a karshen makon da ya gabata. Najeriya ta yi asarar gangunan danyen mai dubu 270 a watan Maris, kamar yadda alkalumman kungiyar OPEC din suka nuna. OPEC ta ce gaba daya, mambobinta 13 na samar da gangunan mai miliyan 28 da dubu 60 a kowace rana a cikin watan da aka yi la’akari da shi wajen yin wannan rahoto. Ta ce an samu karuwar danyen man da ake samarwa a Saudiyya, Angola da Iran, a yayin da aka samu akasin haka a Iraq da Najeriya AMINIYA