NAHCON Ta Yi Jimamin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ƙarƙashin jagorancina, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ta bi sahun sauran al’ummar Najeriya wajen jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari. Wannan rashin ya zo ne a daidai lokacin da ƙasa ke cikin alhini na rashin wani fitaccen attajiri kuma mai jinƙai, Alhaji Aminu Dantata. Wannan al’amari wani tunatarwa ne gare mu duka kan cewa kowa yana da lokacin tafiyarsa, kuma yana ƙara bayyana wa matasa bukatar shiryawa don karɓar ragamar shugabanci na gaba da gina rayuwa bisa gaskiya, amana, hangen nesa da kyakkyawar manufa ga makomar Najeriya. Dukkan su biyu, kowannensu da irin nasa salo, sun kasance tamkar madubin darussa da matasa za su duba su dauki darasi domin gina ingantacciyar ƙasa. Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari ya shahara wajen tsantsar gaskiya, rikon amana da ladabi – wanda ya sanya ya zama abin ƙauna da koyi ga talakawa da dama. Haka kuma, Alhaji Aminu Dantata ya shahara da hikimar kasuwanci da arziki wa...