Shugaban NAHCON Ya Yabawa Gwamnan Imo Bisa Tallafawa Maniyyatan Jahar
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON a yau ta karbi bakuncin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda ya kai ziyarar ban girma a gidan alhazai dake Abuja. A sanarwar da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace A jawabinsa na maraba, Malam Jalal Ahmad Arabi ya bayyana jin dadinsa da karbar bakuncin Gwamnan Jihar Imo a gidan Hajji. Arabi ya bayyana Gwamna Uzodinma a matsayin wani ginshikin tallafi ga Hukumar tare da bayyana yadda ya yi kokarin ganin alhazan jihar sa da ke da niyyar shiga aikin Hajjin bana. A cewarsa, “Kun kasance ginshikin goyon bayanmu a Hukumar ta hanyar goyon bayanku na ganin cewa Musulmin Jihar Imo sun samu damar shiga aikin Hajji. Kun tallafa mana a 2023 da ma bana duk da kasancewar kiristanci ne kuma jihar Imo jihar ce mafi rinjayen Kirista. A gare mu ku alama ce ta zaman lafiya tare da addini da hadin kai a kasar." Ya kuma baiwa Gwamna Hope Uzodinma takardar yabo da lambar yabo ta 🥈 f nagari bisa goyon bayansa