Posts

Showing posts with the label Karamar Sallah

Eid-El-Fitr: Gwamna Yusuf ya taya al'ummar Musulmi murna

Image
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Yusuf ya mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmi da sauran al’ummar Kano bisa samun nasarar kammala azumin watan Ramadan, tare da taya su murnar zagayowar ranar Sallah. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya jaddada muhimmancin kiyaye kyawawan halaye na tausayi, karamci, da'a, kishin kasa, da zaman tare da juna da aka sanya a cikin watan Ramadan. “Yayin da watan Ramadan ya zo karshe, kuma aka ga jinjirin watan Shawwal, ka’idojin tausayi, karamci, horo, kishin kasa, da zaman lafiya da ya sanya ya kamata kowa da kowa ya rungumi shi domin ci gaban al’ummar da muke fata baki daya”. Ya bukaci al’ummar Kano masu girma da su rika rokon Allah ya basu jagoranci a dukkan bangarori. Gwamna Yusuf ya yi wa al’ummar Kano alkawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da ingantattun tsare-tsare don samar da zaman lafiya da hadin kai ga kowa da kowa. “Kwanakun alÆ™awarin suna jiran al’ummar Kano saboda gwamnati m

Labari Da Dumiduminsa: An Wa Watan Sallah A Saudiyya

Image
  Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023. An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana, hakan na nufin Saudiyya ta kammala azumin Ramadan 29. Gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

Abu bakwai da ya kamata ku yi don tafiya sallar Idi

Image
Sallar Idin ƙaramar salla Ibada ce da Allah Ya shar'anta a matsayin kammala Ibada ta azumin watan Ramadan. Sallar Idi na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin musulunci wadda ake yi sau biyu a shekara wato, ƙaramar salla da babbar salla. Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin. Dakta Muhammad Nazifi Inuwa wani malamin addini ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi. Wankan Idi Wankan Idi ɗaya ne daga cikin wanka na sunnah a addinin musulunci wanda ake yi sau biyu a shekara. Dakta Muhammad Nazifi Inuwa ya ce an so duk mai tafiya masallacin idi ya gabatar da wankan Idi, domin dacewe da sunnah. Dangane da wankan, dakta Nazifi ya ce mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan. Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na saura