NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi na kusan naira biliyan biyar
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeroiya NDLEA ta ce ta kama wasu miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya kai naira biliyan biyar a wani gidan ajiye kayyaki.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta gano tan bakwai na tabar wiwi a jihohin Legas da Borno da Edo da Enugu da Katsina da kuma birnin tarayya Abuja.
Hukumar ta ce daga cikin miyagun ƙwayoyin da ta gano sun haɗar da ƙwayar tramadol da yawanta ya kai 3,264,630, da kwalaben kodin 3,490 da wasu ƙwayoyin.
Yayin da yake yaba wa jami'an na NDLEA bisa wannan namijin ƙoƙari, shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi kira a gare su da su ƙara tsage dantse domin kawo raguwar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.