Posts

Showing posts with the label Karin tallafi

Gwamnatin Kano Ta nemi ƙarin tallafin haɗin gwiwa daga Gwamnatin Burtaniya.

Image
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi karin hadin kai da goyon baya daga gwamnatin Burtaniya. A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace, Gwamnan ya yi wannan roko ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Mista Richard Montgomery a ziyarar ban girma a ofishinsa a ranar Talata. Ya ce bangarorin irin wannan alakar hadin gwiwa da ake bukata sun hada da Ilimi, Lafiya, Noma, gyare-gyaren hukumomi, sauyin yanayi da kuma sauye-sauyen zamantakewa. Sauran wuraren da gwamnan ya bayyana sun hada da kiwon lafiya da ilimin mata da yara da kuma masu bukata ta musamman (Nakasassu). Gwamnan ya kuma bayyana matukar bukatar gwamnatin Birtaniya ta ci gaba da zuba jari a jihar domin Kano na bukatar karin masu zuba jari da masana'antu daga kasashen waje. Da yake tunawa da dorewar dangantakar da ke tsakanin Kano da gwamnatin Burtaniya, Gwamna Yusuf ya yaba da irin goyon baya...