Saudiyya Ta Yi Wa Messi Tayin Ninkin Albashin Ronaldo
Kungiyoyin kwallon kafa a kasar Saudiyya na zawarcin gwarzon dan wasan duniya, Lionel Messi, na kungiyar PSG, da tayin albashin da ya zarce na kowane dan wasa a duniya. Rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke zawarcin Messi a Saudiyya ta yi masa tayin albashin Naira biliyan 183.5 (Dala miliyan 400) a shekara, idan kwantaraginsa ya kare da PSG a wata mai zuwa. Kafar labarai ta Telegraph ta kasar Birtaniya ta ce dan wasan ya fara tunanin duba tayin kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da Kyaftin din na kasar Argentina kan kwangilar da take masa tayi, bayan dakatarwar da PSG ta yi masa. Idan hakan ta tabbata, Messi zai rika karbar kusan ninki biyun albashin babban abokin hamayarsa Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu Al Nassr ta kasar Saudiyya ke biyan sa Naira biliyan 96.3 Dala miliyan 210 a shekara, zuwa 2025. A halin yanzu dai, Cristiano Ronaldo ne dan wasa mafi albashi a duniya, inda Messi ke biye da shi, kafin Kylian Mbappe na Farasan da PSG. Wannan sabuwar ta taso ne bayan d