LABARI DA DUMIDUMINSA : Gobara ta tashi a Hedikwatar 'yan sanda ta Kano

Hedkwatar ‘yan sandan Kano da ke Bompai a karamar hukumar Nasarawa, tana cin wuta, inda ake zargin ta kona ofisoshi da muhimman bayanai da dama.

 Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce tuni ta tura jami’an ta wurin da lamarin ya faru domin dakile gobarar da ta tashi a ginin bene mai hawa daya na rundunar.

 Rahotanni da basu tabbata ba sun nuna cewa gobara ta tashi ne a saman benen, Inda ta kama ko’ina amma banda ofishin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda.


Ko da Majiyarmu ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta wayar hannu, mun sami wayarsa a kashe har lokacin haÉ—a wannan rahoton, amma har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki