Gwamnatin Tarayya Da Gwamnonin 36 Sun Shiga Yarjejiniyar Sayar da Kamfanonin Wuta 5

 


A wata sanarwa da darekta janar na ofishin sayar da kaddarorin gwamnati wato BPE Alex Okoh ya fitar, ya nuna cewa za a sayar da kamfanonin wuta biyar a kwatan farko na wannan shekara da muka shiga, domin samar da kudade da za a cike gibin Kasafin kudin shekara 2023 da su.

Kasafin kudin na Naira Triliyan 21.82 ya zo da gibi har na kusan Naira triliyan 11 saboda rashin kudin shiga, haka ya sa aka samu gibin kashi 4.8 a ma'unin arzikin kasar wato GDP, wani abu da masanin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati ya nuna damuwa akan batun sayar da kamfanonin yana cewa akwai abin dubawa a wannan batun sayar da kamfanonin nan domin kar a sake fadawa cikin halin kakanakayi.

  • https://alheekmah.blogspot.com/2023/01/labari-da-dumiduminsa-yusuf-babangida.html
  • https://alheekmah.blogspot.com/2023/01/obasanjo-ya-zama-tamkar-dan-bakin-ciki.html

Mikati ya ce haka aka sayar da kamfanoni ga wadanda ba su da kudi a zamanin gwamnatin da ta shude, har suka gagara ba kasa wadataccen wuta. Mikati ya ce ya yi mamakin wai bankin UBA ne za sayar wa da kashi 60 na kamfanonin inda ya kira da a duba lamarin da idanun basira.

Kamfanonin da ke samar da wutan lantarki ( GENKOS) wadanda za a sayar sun hada da tashar wutar lantarki ta Geregu, da cibiyar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 562 a Calabar Jihar Kros Ribas da kuma cibiyar wutar lantarki ta Olorunsogo, amma ga mai fashin baki a al'amuran zamantakewa da gudanar da mulki Dokta Abdulrahaman Abu Hamisu ya ce wannan ya zo masa da mamaki domin ya kamata Najeriya ta yi damokradiya da gaske.

Abu ya ce matakin da ake dauka bai dace ba domin yana ba sai an sayar da kaddarori kafin a cike gibin kasafin kudi ba.

Abu ya ce ya kamata Najeriya ta yi koyi da wasu kasashe da suka cigaba wajen karban haraji maimakon sayar da kaddarori. Abu ya koka da yadda ake sace kudaden kasa ba tare da an kamo barayin ba. Ya kara de cewa idan ba a hanzarta samo hanyoyin kudaden shigowa ba, to da sauran rina a kaba, musamman yanzu da ake shirin zaben sabon gwamnati.

To sai dai ga tsohon mai ba ministan makamashi shawara a harkar gudanarwa, Idris Mohammed Madakin Jen yana mai ganin an dauki mataki mai kyau da zai kawo wa kasa wutar lantarki.

Idris ya ce dama kudaden na jihohi da kananan hukumomi ne, kuma lokaci ya yi da za a basu abinsu. Idris ya ce bankin UBA ce ta samo masu hannu da shuni da za su saye kamfanin samar da wutan lantarki musamman na birnin taraiyya Abuja.

Majalisar kula da harkokin kasuwanci ta kasa NCP ta amince da tsarin gudanar da aikin gina wani katafaren kamfani na dalar Amurka biliyan 3 da zai samar da wutan lantarki mafi girma a Afirka ta Yamma.

VOA

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki