Posts

Showing posts with the label Fadar Shugaban kasa

Buhari Zai Bar Najeriya Fiye Da Yadda Ya Same Ta – Fadar Shugaban Kasa

Image
  Fadar Shugaban Kasa ta ce a fannin tsaro da habaka tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015. Kakakin Shugaban, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels ranar Talata. Ya kuma ce karyata batun cewa a tsawon mulkin Buhari na shekara takwas, ya nuna kabilanci wajen nafin wadanda za su shugabanci hukumomin tsaron kasar nan. A cewarsa, nadin nasu ba shi da wata alaka da addinin, yanki ko kabilar da mutum ya fito wajen nadinsu, an fi la’akari da cancanta tun da dai doka ta ba Shugaban ikon nada duk wanda ya ga dama. Dangane da batun cewa an fi kashe mutane masu yawa a mulkin Buhari fiye da a shekarun baya duk da cewa bangaren tsaro na cikin manyan abubuwan da ya yi alakawari a kansu, Femi Adesina ya ce ba gaskiya ba ne. Ya ce, “Ka san cewa akwai wani rahoto da ya ce an fi samun karancin mutanen da aka kashe a 2022 a cikin shekara 12 da suka gabata a sakamakon ayyukan ta’addanci? Mun fa sani

Akwai Makiyan Tinubu A Fadar Shugaban Kasa – El-Rufa’i

Image
  Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai makiyan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Shugaban da suke kokarin ganin sun kai shi kasa. Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na  Sunrise Daily  da safiyar Laraba. El-Rufa’i ya ce mutanen, wadanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani na APC. Ya kuma ce mutanen na fakewa da bukatar ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace. Ya ce, “Na tabbatar a cikin Fadar Shugaban Kasa akwai masu son mu fadi zaben nan, saboda bukatarsu ba ta biya ba, an kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani. “Wadannan mutanen na kokarin fakewa da bukatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu; wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Najeriya ta kashe makudan kudade abu ne da dukkanmu mun dade da amincewa a cire shi. “Sai da ma na tattauna da Shugaban Kasa a kan

Obasanjo ya zama tamkar dan bakin ciki - Fadar Shugaban kasa

Image
Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taɓa daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baƙin ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ƙasa ba. Fadar shugaban ƙasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alƙawura a kanta. Haka kuma fadar shugaban ƙasar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ƙarya domin ya samu ƙuri'unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ƙuri'unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar. Fadar shugaban ƙasar ta kuma ce Obasanjo yana baƙin ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da'awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe fiye da wanda